Fada ya ricabe a Somaliya

Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Mayakan Al-Shabbab na ci gaba da kai hare-hare

Kazamin fada ya rincabe a tsakiyar kasar Somaliya tsakanin mayakan kungiyar Al-Shabaab da kuma dakarun kasar Habasha.

Kungiyar Al Shabaab ta ce ta hallaka 'yan kasar Habasha da ke cikin dakarun kungiyar tarayyar Afirka -- tare da lalata motocin soji bakwai.

Mazauna kauyen Jame'o da ke kusa da kauyen Bur Hakaba -- sun ce sun ji karar manyan makamai.

Har yanzu dai babu wani martani daga 'yan kasar ta Habasha.

An fatattaki mayakan na Al-Shabaab daga akasarin garuruwan kasar ta Somaliya, amma kuma suna rike da ikon yankunan wajen kasar da dama.