Zimbabwe za ta daina amfani da kudin kasar

Image caption Kudin kasar Zimbabwe

Zimbabwe ta soma kawo karshen amfani da takardun kudin kasar, inda za a koma amfani da kudaden kasashen waje domin hada-hadar yau da kullum.

A Zimbabwe dai ana amfani da kudaden kasashen waje kamar dalar Amurka da kuma kudin Afirka ta kudu, wato Rand tun daga shekara ta 2009.

Daga yanzu za a dinga sayar da kudin kasar ne kawai a matsayin wata haja.

Amma daga ranar Litinin za a fara musayar kudin kasar da dala inda za a ringa sayar da sama da dalar Zimbabwe biliyan 4,000 a kan dalar Amurka biyar.

An dade ana kai ruwa rana kan wannan matakin sai dai gwamnan babban bankin kasar John Mangudya, ya bayyana cewa ba zai yiwu a dinga amfani da kudade biyu a kasar ba, don haka akwai bukatar a kimanta kudin da za a yi amfani da shi, ko kuma yin amfani da dalar Amurka a Zimbabwe.