Mun amince da Saraki-APC

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Shugaban Majalisar Dattijai a Najeriya, Bukola Saraki

A yayin takaddamar cikin jam'iyyar APC a Najeriya ke ci gaba da dumama sakamakon zaben shugabannin majalisun dokokin kasar, uwar jam'iyyar ta ce ta amince da zaben da aka yi wa Sanata Bukola Saraki a matsayin shugaban majalisar dattawa.

Shugaban jam'iyyar na kasa Mista John Oyegun ya ce jam'iyyar bata da zabi illa ta amince da Sanata Saraki a matsayin shugaban majalisar, tunda dai kakwarorinsa a majalisar ne suka zabe shi.

Sai dai ya ce 'yan majalisar dattawan da suke barazanar zuwa kotu kan batun suna da 'yan cin yin haka.

Mista Oyegun wanda ya ce jam'iyyar ta APC zata shawo kan kalubalen da take fuskanta, ya ce suna ci gaba da tattaunawa yadda za a ciyar da jam'iyyar gaba.

Abinda ya rage a gani shi ne, shin suma 'ya'yan majalisar dattawan da suka ja daga a kan basu amince da Sanata Bukola Saraki a matsayin shugabansu ba za su bi sahun uwar jam'iyyar?