Buhari ya tafi Afrika ta Kudu

Hakkin mallakar hoto Getty

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya tafi Afrika ta Kudu domin halartar taron kungiyar Tarayyar Afrika, wanda za a fara ranar Lahadi.

An tsara cewa zai shugabanci taron kwamitin tsaro da zaman lafiya na kungiyar, wanda Najeriya ke jagoranta.

Sanarwar da mai baiwa shugaban Najeriyar shawara kan harkar yada labarai ya bayar ta ce Shugaba Buhari zai nemi hadin kan kungiyar Tarayyar Afrikan wajen yakar Boko Haram a Najeriya da makwabtanta.

Wasu 'yan Najeriya dai sun ce kamata ya yi shugaban ya zauna gida ya fusakanci matsalolin da suka addabi kasar kai-tsaye, maimakon tafi-tafiyen da ya ke.

To amma a hirar da ya yi da Sashen Hausa na BBC, jami'in kula da yada labarai na shugaban kasar, Malam Garba Shehu, ya ce zuwa taron na Tarayyar Afrika na da muhimmanci sosai ga Najeriya.

Karin bayani