Hillary Clinton ta yi gangami a New York

Hakkin mallakar hoto BBC World Service

'Yar takarar da ke gaba-gaba ta jam'iyyar Democrat a neman kujerar shugabancin Amurka, Hillary Clinton, ta gabatar da babban jawabinta na farko a wani gangamin da ya sami halartar dubban magoya bayan jam'iyyarta a birnin New York.

Da take jawabi a wurin shakatawa na tsibirin Roosevelt, 'yar takarar ta maida hankali ne akan batun tattalin arziki.

Hillary Clinton ta ce cigaba na hakika ya kamata ne a hadu baki daya wajen raya shi sannan kuma kowa ya amfana.

Ta ce: "Kyautatuwar rayuwa ba ta manyan shugabanni ba ce da manajojin cibiyoyin kasuwanci, dimokradiyya ba ta hamshakan attajirai ba ce kadai. Ku ma kuna da hakki a ciki, ku ne ku ka dawo da kasar mu kan tafarki, saboda haka yanzu lokacin ku ne ku tabbatar da dorewar wannan nasara a kuma cigaba.

"Wannan shine dalilin da ya sa na fito takarar shugabancin Amurka."

Mijinta, tsohon shugaban kasa Bill Clinton, da kuma 'yarta Chelsea duk sun halarci gangamin.

Karin bayani