Za a binciki kudaden kwallo da suka bace a Ghana

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption 'Yan wasan Ghanan ba su taka rawar gani ba a Brazil 2014

Gwamnatin Ghana ta yi kira da a gudanar da wani bincike kan hukumar kwallon kafar kasar, game da zarge- zargen cewa wasu miliyoyin daloli na kudaden gasar cin kofin duniya sun yi layar zana.

Hukumar kwallon kafar Ghana ta musanta cewa an samu matsalar cin hanci da rashawa gabanin gasar cin kofin shekarar 2014 a Brazil

Gwamnatin Ghanan dai na maida martani ne ga wata hukumar bincike da aka kafa, domin ta yi nazari akan gazawar da Ghanan ta yi a gasar, a lokacin da 'yan wasan Black Stars suka gaza lashe koda wasa daya tal.