Jamus na maraba da 'yan gudun hijira

Image caption Turai na fuskantar matsalar yawan 'yan gudun hijira saboda yaki a kasashensu

Jami'an Jamus sun ce yawan 'yan gudun hijirar dake kara kwararowa daga kasashe irinsu Sryria ka iya taimakawa wajen cike gurbin karancin masu aikin hannu a cikin kasar.

Shugaban hukumar daukar ma'aikatan Jamus ya fadawa wata jarida cewa, a mafiyawancin lokuta akan sami mutanen dake tserewa rikicin Syria suna da ilmi , don haka Jamus ta na matukar maraba dasu

Jamus na karbar takaddun masu neman mafaka fiye da kowacce kasa a nahiyar Turai.

Gwamnatin Jamus din ta yi kiyasin cewa ko a wannan shekaarar 'Yan gudun hijira dubu- 400 ne zasu nemi mafaka a Kasar.