An sake yi wa Amurka kutse

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Masu kutse cikin kwamfuta

Wasu masu satar bayanai a kwamfutoci da ake alakantawa da China sun yi kutse cikin wasu muhimman bayanan miliyoyin jami'an soji da masu leken asiri a Amurka.

Ana ganin wasu daga cikin bayanan da aka sata, zasu iya jefa jami'an cikin hadarin batanci.

Wannan shi ne al'amarin kuste na biyu da Amurka ta fuskanta daga wasu da take alakantawa da China.

Jaridar Washington Post da ake bugawa a Amurka, ta ce masu bincike suna duba kutsen da aka yi cikin runbum adana bayanan gwamnatin Amurka har sau biyu a dan tsakanin nan.

Rahotanni sun ce a daya daga cikin kutsen, masu satar bayanan sun samu taba bayanan ma'aikata miliyan 14 da suka hada da wadanda suka bar aiki, ba miliyan hudu ba kamar yadda aka sanar a cikin makon jiya.

Rahotannin sun ce rumbun bayanan na biyu da aka yi wa kusten, ya kunshi bayanan hada hadar kudi da suka shafi masu neman ayyukan yi.

Bayanan kuwa sun hada da na neman sanin ko masu neman aikin suna da tabin kwakwalwa, ko kuma suna mu'amala da kwayoyi, ko an taba kama su a baya saboda wani laifi, da bayanai a kan 'yan uwansu.

China dai ta yi watsi da zargin da Amurkan ta ke mata akan cewa tana da hannu a lamarin.