'Yan Boko Haram su kai hari Babban Gida

Hakkin mallakar hoto BOKO HARAM
Image caption Mayakan kungiyar Boko Haram

A Najeriya, rahotanni daga karamar hukumar Tarmowa ta jihar Yobe na cewa wasu da ake zargin 'yan kungiyar Boko Haram ne sun afka Babban Gida da safiyar Lahadin nan, inda suka yi ta harbe harbe da kone kone.

Mazauna garin da suka tsere cikin daji saboda harbe harben sun shaidawa BBC cewa tun a daren Asabar suka samu labarin maharan na shirin afkawa garin.

Sai dai hanyoyin sadarwa na mazauna garin Babban Gida da suka sanar da BBC halin da suke ciki sun yanke, mai yiwuwa saboda suna cikin daji.

Kawo yanzu hukumomi a Najeriya basu ce komai ba game da harin, amma wani dan jarida a Yobe ya tabbatar wa BBC da faruwar lamarin.