ICC ta nemi a kama Al-Bashir a Taron Afirka

Hakkin mallakar hoto AFP Getty Images
Image caption An zargi Omar Al-Bashir da aikata laifukan yaki a Darfur

Kotun hukunta manyan laifuka ta duniya ta yi kira ga Afirka ta Kudu data kama Shugaban Sudan Omar al Bashir, wanda ya isa kasar domin halartar taron Kungiyar Tarayyar Afirka, wanda za'a bude yau Lahadi

A wata sanarwa data fitar, kotun ta ICC tace har yanzu akwai takaddun neman kama shugaban dake aiki akansa.

A matsayinta na mamba ta ICC, hakki ne da ya rataya akan Afirka ta Kudun ta tsare Mr. Bashir da zarar ya taka kafarsa cikin kasar.

Sai dai a baya Tarayyar Afirkan ta ki bai wa kotun ICC hadin-kai, ta na zargin cewa Kotun na yiwa shugabannin kasashen Afirka bita da kulli.