Jirgin sama jannati Philae ya farfado

Hoton jirgin sama jannati philae Hakkin mallakar hoto EPA
Image caption Hoton jirgin sama jannati philae

Shi dai jirgin sama jannatin wanda aka yiwa lakabi da Philae ya shafe tsawon watanni bakwai ba'a ji duriyarsa ba.

Cibiyar nazarin sararin samaniya ta tarayyar turai ta ce kumbon sama jannatin yana yin abin da ya kamata kuma cikin shirin cigaba da ayyukansa.

Ya daina aiko da sakonni ne 'yan sa'oi kadan bayan da ya sauka akan tauraruwar mai wutsiya wato comet a bara.

McCork-ran babban jami'i mai bada shawara kan harkokin kimiyya a cibiyar nazarin sararin samaniya ta tarayyar turai yace ya yi farin ciki matuka baturan da aka sanyawa na'urar ya yi chaji kuma zai cigaba da aiki