Za a yanke hukunci a kan kama Al-Bashir

A ranar Litinin din nan ne wata kotu a Afirka ta Kudu za ta yanke hukunci a kan ko kasar za ta mika shugaban kasar Sudan Omar Al-Bashir ga Kotun Hukunta Manyan Laifuka, ICC.

Shugaba Al-Bashir -- wanda ya ke kasar Afirka ta Kudun yanzu domin taron kungiyar kasashen Afirka-- yana fuskantar tuhume-tuhume a gaban kotun ta ICC bisa zargin aikata laifukan yaki da kisan kare-dangi.

A ranar Lahadi ne wani alkali a kasar ya hana shugaba Al-Bashir fita daga kasar har sai an saurari wata kara da aka shigar da ke neman a kama shi.

Sai dai abu ne mawuyaci kasar Afrika ta kudu ta kama shugaba Al-Bashir duk da cewa kasar za ta iya yin hakan a matsayinta na mamba a kotun.

Ana sa ran lauyoyin da ke wakiltar gwamnati za su bukaci babbar kotu a kasar da a bar shugaba Al-Bashir ya koma kasarsa.

Lauyoyin za su shaida wa kotun cewa kungiyar kasashen Afirka ce ta gayyaci shugaba Albashir, don haka kasar ba ta da hurumin tsare shi.

Karin bayani