Boko Haram ta addabi garin Blame

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Mayakan Boko Haram na ci gaba da addabar kasashen Nigeria da Nijar da Kamaru

Mutanen garin Blame na Jamhuriyar Kamaru sun fara tserewa sakamakon samamen da wadanda ake zaton 'yan Boko Haram ne ke kai wa a garin.

Mayakan sun sace awaki masu dimbin yawa da wayoyin hannu a garin.

Da dama daga cikin mazauna garin da ke tserewa suna komawa ne birnin Kouseri da zama.

Tun ranar Larabar makon jiya ne mayakan kungiyar ta Boko haram suka kai hari a garin na Blame.

Sai dai ba a samu asarar rayuka ba a harin.