Buhari zai kai ziyara a Kamaru

Hakkin mallakar hoto
Image caption Buhari ya gana da Issoufou da Deby da kuma Boni Yayi a Abuja

Shugaban Nigeria, Muhammadu Buhari yana shirin kai ziyara kasar Kamaru da zummar hada kai da kasar domin yaki da kungiyar Boko Haram.

Shugaba Buhari ya kai ziyara a Nijar da Chadi a makonsa na farko da kama aiki, kuma ya ce ya so ya je Kamaru ba da dan taron da ya halarta na kasashen da suka fi karfin tattalin arziki a duniya, G7 a Jamus ba.

A makon jiya ne, shugaba Buhari ya gana da takwarorinsa na Nijar da Chadi da kuma Benin a wani taro da suka yi a Abuja, sai dai shugaban Kamaru, Paul Biya bai je wurin ba, koda-yake ministan tsaron kasar ya wakilce shi.

Kasashen biyu dai ba sa ga-miciji da juna musamman takaddamar da suke yi kan iyaka.

Sai dai kamfanin dillacin labarai na AFP ya ambato shi a wajen taron kasashen Afirka da ake yi a Afirka ta kudu yana cewa "idan na koma Najeriya, zan yi kokarin zuwa Kamaru".

Shugaban Buhari ya sha alwashin hada gwiwa da makwabtan kasarsa domin murkushe kungiyar ta Boko Haram, wacce ta kashe dubban mutane.