An gano gawarwaki cikin hamadar Nijar

Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Matsalar 'yan cirani daga kasashen Afira zuwa nahiyar Turai na kara ta'azzara

Kungiyar kula da kaurar jama'a ta duniya, IOM, ta ce an gano gawarwakin wasu mutane 18 a cikin hamadar arewacin Jamhuriyar Nijar.

Dukkanin mutanen 'yan asalin wasu kasashen Afrika ta yamma ne, da suka yi kokarin ketara hamadar domin isa kasashen Turai.

Dubban mutane ne dai kan yi wannan yunkuri na ketara hamadar, da nufin kai wa gabar tekun Libya, inda suke fatan yin wata tafiyar mai hadari domin ketara tekun Bahar Rum.

Kasashen Turai dai sun yunkuro domin takawa matsalar birki a 'yan kwanakin nan.