Kurdawa sun yi wa Tal Abyad kawanya

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Mayakan Kurdawa

An ba da rahoton cewa mayakan Kurdawa sun yi wa birnin Tal Abyad da ke arewa maso gabashin kasar Syria inda da mayakan IS ke rike da iko kawanya.

Mayakan na IS sun tarwatsa gadoji biyu na shiga birnin, don hana mayakan Kurdawan kutsawa.

A kwanakin baya-bayan nan, duban fararen hula ne suka tsere daga fadan da ake gwabzawa, inda suka tattaru a tsallaken kan iyakar kasar Turkiyya.

Mahukuntan kasar Turkiyyar sun bar wasu daga cikin 'yan gudun hijirar sun ketara kan iyakar ranar Lahadi.

Garin na Tal Abyad na da matukar muhimmanci ga mayakan na IS, saboda a nan ne ake da wata babbar hanya da ake bi wajen shigar da kayayyaki zuwa hedkwatar kungiyar da ke Raqqa.