Direbobin tirela sun rufe hanyar Zaria

Image caption Direbobin sun yi zargin cewa wani soja ya harbi abokin aikinsu.

Direbobin motocin tirela a jihar Kaduna da ke Najeriya sun rufe hanyar Kaduna zuwa Zaria sakamakon zargin da suka yi cewa wani soja ya harbi abokin aikinsu.

Rahotanni dai na cewa sojan ya harbi direban a kafarsa ne ranar Lahadi da daddare bayan ya hana shi cin hanci.

Rahotannin sun ce yanzu haka dai direban na can kwance a asibitin, inda yake samun kulawa sakamakon harbin.

Lamarin ya harzuka direbobin manyan motoci, kuma hakan ne ya sa suka rufe hanyar da ta tashi daga Kaduna zuwa Zaria ta daidai unguwar Dankande domin nuna fusatar da suka yi.

Direbobin sun ce ba za su bude hanyar ba sai gwamnan jihar, Malam Nasir El-Rufai ya je wajen domin su bayyana masa irin cin zarafin da jami'an tsaro ke yi musu.

Har yanzu dai jami'an tsaro ba su cewa komai game da batun ba.

A Najeriyar dai, an sha fuskantar irin wannan matsala, lamarin da kan kai direbobin manyan motocin na rufe hanyoyi, kuma hakan kan yi sanadiyar kuntata wa mutane.