Bam ya hallaka mutane 8 a Potiskum

Hakkin mallakar hoto BOKO HARAM
Image caption 'Yan Boko Haram sun saba kai hare-hare a garin na Potiskum.

Wasu 'yan-kunar-bakin-wake sun kai hari a garin Potiskum na jihar Yobe da ke Nigeria, lamarin da ya yi sanadiyar mutuwar mutane da takwas.

Shaidu sun gaya wa BBC cewa an kai harin ne a wurare biyu, a titin Ningere da kofar Sarkin Baka.

Sun kara da cewa maharan sun kunna kai cikin jama'a, lamarin da ya yi sanadiyar mutuwar akalla mutane 12.

Dan kunar bakin wake na farko ya tayar da bam din da ke jijkin sa ne a wani wuri da ake kira masha gabas da dorawa a Potiskum.

Bayanai sun nuna kusan a daidai wannan lokaci kuma, wani dan kunar bakin waken ya tayar da na sa bam din a hanyar wani gidan mai kusa da gidan Sarkin baka.

Har yanzu dai babu bayani daga jami'an tsaro kan lamarin.

'Yan kungiyar Boko Haram sun saba kai hare-hare a garin na Potiskum da ma wasu yankunan arewacin Najeriya.

Sabon shugaban kasar, Muhammadu Buhari ya sha alwashin kawar da kungiyar Boko Haram wacce ta hallaka mutane fiye da 15,000 a cikin shekaru shida a Nigeria.