Sakkowar 'yan sama jannati duniyar Earth

Image caption Samantha Cristoforetti

Wasu 'yan sama jannati 3 da suka shafe akalla watanni 7 a cikin falaki, na kan hanyar su ta dawowa doron kasa bayan da jirgin su ya bar tashar sararin samaniya ta duniya.

A cikin watan jiya ne ya kamata su dawo, amma sai suka dakatar da hakan bayan da jirgin dake kai musu kaya ya kone lokacin da ya shigo sararin duniyar Earth.

Jinkirin da aka samu na nufin cewa daya daga cikin 'yan sama jannatin, ta kafa wata bajinta ta duniya na kwanaki mafi yawa da wata mace ta taba kwashewa a tafiya guda a sarari samaniya.

Frank De Winne na hukumar binciken sararin samaniya ta Turai ya ce jinkirin ya sa zata kafa bajinta.

Ya ce "wannan yana da muhimmanci, farko ga hukumar binciken sararin samaniya ta Turai, kuma wannan mata, Samantha Cristoforetti daga hukumar binciken sararin samaniya ta Italiya ta shafe kwanaki 210 a sararin samaniya.

Ana sa ran kumbon zai sauka ne a kasar Kazakhstan.