Saudiyya ta bude kofarta ga 'yan kasuwa

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Harkokin kasuwanci a Saudiyya tare da kasashen waje za su bude

Kasuwar hannayen jarin Kasar Saudiyya za ta bude kofarta ga wasu masu zuba jari 'yan kasashen waje, wadanda daga yau Litinin zasu iya sayen hannun jari a kamfanonin da ake hada- hadar kasuwanci dasu a kasuwar hannun jarin kasar

Za'a takaita 'Yancin sayen hannun jari ga 'yan kasuwa masu zuba jari da aka amincewa, sannan za'a samu iyaka na irin jarin da za'a zuba

Amma wakilin BBC kan tattalin arziki ya ce arzikin man da Saudiyya take da shi, na nufin ta na da wadatar tattalin arzikin da zata tabbatar da cewa wasu masu zuba jari zasu samu damammaki