An musanta kashe Belmokhtar

Hakkin mallakar hoto
Image caption An sha ba da rahoton kashe Belmokhtar

Wata kungiyar 'yan gwagwarmaya a Libya mai suna Ansar al-Sharia ta fitar da sunayen wasu masu fafatuka su bakwai da ta ce an kashe a karshen mako.

Ta ce an kashe su ne sakamakon hare-hare ta sama da Amurka ta kai da jirgi marar matuki.

Sai dai a cikin jerin sunayen babu jagoran mayakan sa-kai na Islama, Mukhtar Belmokhtar.

A Litinin ne aka ambato wani kakakin ma'aikatar tsaron Amurka yana cewar suna da tabbacin cewa an kashe Belmokhtar, mutumin da ake cewa shi ya jagoranci mummunan harin da AlQaeda ta kai a 2013, a wata masana'antar sarrafa iskar gas ta Aljeriya.

Daga bisani ma'aikatar tsaron Amurka ta ce tana sake nazari kan shaidun da take da su.

A baya dai an sha ba da labaran kashe Belmoktar daga baya a ce kuskure ne ba shi ba ne.