Jirgin kasa ya yi karo da tirela a Tunisia

Image caption Taswirar Tunisia

A kalla mutane 17 sun mutu kuma mutane 70 sun samu raunika bayan da jirgin kasa mai dauke da fasinjoji ya kara da tirela a Tunisia.

Lamarin ya faru ne a garin El Fahes, wande ke da nisan kilomita 60 a kudu maso yammacin Tunis, babban birnin Tunisia da safe a lokacinda jama'a suka fi zirga-zirga.

Wani wanda hatsarin ya faru a kan idon sa, ya ce ya ga tarkacen jirgin da na motar da suka yi karo da kuma gawarwaki a kan hanyar jirgin kasa.

An aike motar daukar marasa lafiya daga makwabtan garin da hatsarin ya faru saboda su dauki wadanda suka samu raunuka.