Bush zai tsaya takarar Shugabancin Amurka

Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Shi ne na uku a danginsu da yanzu yake neman shiga fadar White House

Dan siyasar jami'iyyar Republican a Amurka Jeb Bush ya sanar da cewa yana takarar shugabacin kasar a hukumance

Da yake kaddamar da yakin neman zabensa a Miami, tsohon gwamnan Florida ya gabatar da kansa a matsayin wanda zai kablubalanci abinda ya bayyana da manyan 'yan siyasar Wahington masu takama da kansu

Ya kuma ce a shirye yake ya taimakawa marasa karfi a Amurka

An dai kaucewa sa sunan 'Bush' a alamar yakin neman zabensa, a wani mataki da ake gani cewa yunkuri ne na musamman da yayi, domin nisanta kansa daga dan-uwansa da kuma mahaifinsa, wadanda dukkaninsu tsoffin shugabannin Amurka ne.

Shi ne dan takarar jam'iyyar Republican na 11 dake neman shiga fadar White House.