Nestle zai lalata taliya ta miliyan $50

Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Taliyar Maggi Noodles

Kamfanin Nestle ya ce zai lalata sananiyar taliyar Maggi Noodles, bayanda hukumar sa ido a kan kayan abinci ta Indiya ta hana sayar da taliyar.

Hukumar sa ido a kan kayan abinci ta ce gwajin da aka yi ya gano cewar taliyar Noodles "Zai iya cutarwa kuma yana da hadari" kuma ya zargi Nestle da rashin bin dokokin ingancin abinci.

A cikin wata sanarwa kamfanin ya bayyana cewar darajar taliyar da aka janye sun hada da na kan kanta da kuma wadanda aka ajiye a ma'adanar masana'antar da kuma wadanda suke wurin masu rarrabawa.

Za'a yi la'akari da karuwan bashi, misali kawo taliyar daga kasuwa, dauko su zuwa inda za'a lalata da kuma hasarar kudaden da za'a yi wurin lalata su da dai sauran su.

Kamfanin Nestle ya ce "daga baya za'a iya kayyade adadin kudin".

'Dalma'

A farkon wannan watan, Nestle ya fara janye nau'in taliyar Maggi Noodles daga shaguna bayan da hukumomi suka ce sun gano cewar tana dauke da dalma dayawa a wasu fakiti-fakiti na taliyar.

Kamfanin ya kalubalanci haramcin a babban kotu da ke birnin Mumbai game da dokokin ingancin abinci a kasar Indiya.

Babban jami'in Nestle na duniya, Paul Bulcke ya nemi ya ga sakamakon gwajin kuma ya yi alkawarin mayar da taliyar Maggi a kan kantar shaguna nan da ba da dadewa ba.

Ana ta gwaji a kan noodles din saboda sinadarin monosodium glutamate, wanda aka fi sani da MSG.

An fara samun taliyar noodles a kasar Indiya a shekarar 1983 kuma ana samu a kananan shaguna a fadin kasar.