An gano karin gawarwaki 30 a hamadar Nijar

A cikin kasa da mako guda an gano gawarwaki kusan 50 Hakkin mallakar hoto
Image caption A cikin kasa da mako guda an gano gawarwaki kusan 50

Hukumar kula da kaurar jama'a ta duniya, IOM, ta ce ta gano karin gawarwaki 30 a cikin hamadar arewacin Jamhuriyar Nijar.

Sai dai babu tabbas a kan abin da ya haddasa mutuwarsu.

A ranar Lahadi ma, an gano gawarwaki a wani bangare na hamadar.

Hukumar IOM din ta ce an gano gawarwakin ne a Dirkou da ke arewa maso gabashin Agadez.

Dukkanin mutanen 'yan asalin wasu kasashen Afrika ne, da suka yi kokarin ketara hamadar domin isa kasashen Turai domin kauce wa talauci.

Dubban mutane ne dai kan yi wannan yunkuri na ketara hamadar, da nufin kai wa gabar tekun Libya, inda suke fatan yin wata tafiyar mai hadari domin ketara tekun Bahar Rum.

Kasashen Turai dai sun yunkuro domin takawa matsalar birki a 'yan kwanakin nan.