Karuwar safarar 'yan Nigeria a Biritaniya

Image caption Wasu daga cikin mutanen da ake safararsu, ana tilasta musu yin karuwanci ne

Jami'an gwamnatin Birtaniya sun bayar da rahoton samun karuwar safarar mutane zuwa kasar, inda ake samun galibin wadanda ake safarar daga Najeriya ana tilasta musu yin aiki a matsayin barorin gida ko kuma karuwai.

Alkaluman da hukumomi suka fitar na nuna cewa akwai mutane kimanin 2000 da ake kyautata zaton an yi safarar su ne, wadanda aka kai wa hukumomi rahoto a 2014, ciki har da guda 244 daga Najeriya.

Akwai kuma wasu da ake sa wa ayyukan gona da wadanda ke aiki a kananan jiragen ruwan kamun kifi.

Melisa na daga cikin su.

Tun tana da shekaru 10 mahaifinta ya kawo ta Biritaniya, inda ya mika ta a hannun wata mata da ta yi ta gana mata azaba kafun daga baya ta samu ta gudu.

Ma'aikatar harkokin cikin gida ta Biritaniya ta ce a watan Disamba akwai mutanen da yawansu ya kama daga 10,000 zuwa 13,000 wadanda suka samu kan su a kangin bauta a Biritaniya.