An haramta sa nikabi a Chadi

Hakkin mallakar hoto EPA
Image caption Chadi ta haramta sa nikabi

An haramta saka nikabi a Chadi sakamakon hare-haren da masu tayar da kayar baya suka kai makarantar 'yan sanda da kuma hedikwatar 'yan sanda a wannan makon.

Firai minista, Kalzeube Pahimi Deubetne ya sanar da hakan a ranar Laraba yayin da wasu malaman addini suka kai masa ziyara.

Firai ministan ya ce "Sanya nikabin ko dukkan wani kaya da zai rufe ko'ina na jiki har da ido to yaudara ce, kuma mun haramta hakan daga yanzu."

Ya kara da cewa "Dole ne a daina hakan ko a makarantu ko a duk wani waje na taruwar mutane."

An dai tsaurara tsaro a Ndjamena babban birnin kasar, tun bayan da aka kai harin, wanda gwamnatin kasar ke zargin kungiyar Boko Haram ne ta kai.