Dangote zai gina masana'antu a Jigawa

Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Dangote na gina katafaren kamfanin siminti a jihar Kogi

Shugaban rukunin masa'antun Dangote, Alhaji Aliko Dangote ya ce zai kafa masana'antu biyu a jihar Jigawa da ke arewa maso yammacin kasar.

Masana'antun dai na sarrafa shinkafa da kuma sikari za a kafa su ne a bangaren jihar da ake noman rake da kuma shinkafa a gabashin jihar.

Aliko Dangote ya bayyana cewa "Za mu kashe dala miliyan 250 a wajen gina masana'antun."

Sakamakon haka kuma za a kaddamar da wani gagarumin noma domin samar da abubuwan da za a dinga sarrafawa a masana'antun, wanda haka zai samar da dubban ayyukan yi ga jama'a jihar.

An dai kammala amincewa da wannan yarjejeniya ne a wajen wani taro da aka gudanar tsakanin kamfanonin Dangote da gwamnatin jihar, da kuma masu ruwa da tsaki a jihar ta Jigawa.

Alhaji Aliko Dangote shi ne wanda ya fi kowa arziki a Afrika inda yake da manyan kamfanonin siminti da sikari a kasashe da dama.