Gwamnoni 36 za su gana da Buhari

Image caption Gwamnoni da dama sun kasa biyan albashin ma'aikata

Gwamnonin jihohin Najeriya su 36 sun yanke shawarar tattaunawa da shugaban kasa dangane da halin rashin kudi da wasu jihohin suka tsinci kansu a ciki.

Gwamnonin sun cimmam wannan matsaya a wani taro da suka yi a Abuja babban birnin kasar.

Shugaban kungiyar gwamnonin Nigeria, Abdul'aziz Yari na jihar Zamfara, ya ce za su gabatar shawarwarin da suka cimma a wannan taron ga shugaban kasar yayin taron da za su yi da shi.

"Mun yanke shawarar za mu tattauna da shugaba Buhari domin mu hada karfi da karfe wajen shawo kan matsalolin da suka addabemu," in ji Yari.

Gwamnonin sun tattauna ne kan abin da suka kira kalubalen tattalin arziki da jihohin nasu ke fuskanta musamman yadda za a kawo ma wasu daga cikin jihohin da ba su da kudaden gudanar da ayyuka da biyan albashi dauki.

Jihohi da dama sun shafe fiye da watanni shida basu biya albashin ma'aikata ba saboda faduwar darajar danyen mai a kasuwar duniya.