Hukumar kwastam ta saki kaya a Kano

Image caption Kasuwar Kantin Kwari na daya daga cikin manyan kasuwannin tufafi a nahiyar Afirka

'Yan kasuwar sayar da tufafi ta Kantin Kwari a jihar Kano da ke arewa maso yammacin Najeriya sun ce hukumar hana fasa kwauri ta saki kayan da ta kama musu bisa zargin shigo da kayan ba bisa ka'ida ba.

'Yan kasuwar sun ce hukumar ta kwastam ta ba su damar diban wasu daga cikin kayan, sannan su debi sauran kayan idan 'yan kasuwar suka biya kudin fito.

A watan jiya ne dai hukumar ta hana fasa kwauri ta kama wasu manyan shagunan ajiye kaya da kudinsu ya kai N300bn.

'Yan kasuwar dai sun ce sun shiga mummunan yanayi sakamakon kamen da hukumar ta yi.