Za a rusa gwamnatin Falasdinawa

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Abbas ya ce Hamas ta ki ba shi hadin kai.

Shugaban Falasdinawa ya ce za a rusa gwamnatin hadin-kan da aka kafa tsakanin Hamas da Fatah.

Mahmud Abbas ya shaida wa 'yan kungiyarsa ta Fatah cewa ya zama wajibi a rushe gwamnatin saboda Hamas ba za ta ba su damar yin mulkin yankin Gaza da ke hannunta ba.

A bara ne dai bangarorin biyu suka kafa gwamnatin hadin-kan da zummar kawo karshen barakar da ke tsakanin su, sai dai tun da aka kafa gwamnatin ake fuskantar matsala tsakanin su.

Bangaren Fatah na Shugaba Abbas ne ke iko da yankunan Palasdinawa ciki har da yammacin Kogin Jordan, yayinda Hamas ke iko da Gaza.