Gyara ga dokokin kiyaye zaman lafiya

Dakarun kiyaye zaman lafiya na Majalisar dinkin duniya
Image caption Dakarun kiyaye zaman lafiya na Majalisar dinkin duniya

Wani rahoton Majalisar Dinkin Duniya ya ce akwai bukatar a gudanar da babban garan-bawul ga ayyukan kiyaye zaman lafiya na majalisar.

Rahoton -- wanda aka kaddamar kafin a samu bayanan zargin cin zarafin kananan yara da aka yi a kasashen Haiti da Liberia -- ya ce ya kamata a haramta wa kasashen da aka samu dakarunsu da laifin cin zarafin kananan yaran ba da gudunmuwar sojojinsu ga rundunar.

Rahoton ya ce ya kamata a tube wa sojojin da aka samu da irin wannan laifin rigar-kariya daga tuhuma, kuma za a bukaci kasashensu su bayyana matakan da aka dauka a kan su.

Har wa yau, rahoton ya nemi a gudanar da bincike a kan irin wannan zargi cikin watanni shida.

Karin bayani