Bam ya hallaka mutane 31 a Yemen

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Har yanzu gwamnatin na cikin tsaka mai wuya a Yemen

Mutane akalla 31 ne aka ba da rahoton sun hallaka a wasu jerin fashewar bama-bamai a Sanaa babban birnin kasar Yemen.

An kai harin ne kan wasu masallatai biyu lokacin da musulmai mai gudanar da sallah la'asar.

Daya harin kuma an kai shi ne kan wani ofishin harkokin siyasar 'yan tawayen Houthi.

A baya dai mahukuntan kasar ta Yemen sun zargi 'yan tawayen da tarwatsa wani mai shiga tsakani na gwamnati, wanda ke wajen taron tattaunawar zaman lafiya a birnin Geneva.

Dakarun da kasar Saudiyya ke jagoranta na cigaba da kai hari ta sama kan yanukan yan Houthin.

Mutane fiye da dubu biyu ne suka mutu a cikin makonnin da aka shafe aka tashin hankalin.