Boko Haram ta kashe mutane 38 a Nijar

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Kaashen Najeriya da Nijar da Chadi da Kamaru da Benin sun sha alwashin murkushe Boko Haram.

Hukomomi a Jamhuriyar Nijar sun ce 'yan kungiyar Boko Haram sun kashe a kalla mutane 38 a lokacin da suka kai hari a kauyuka biyu da ke kudancin kasar.

Dan majalisar dokokin da ke wakiltar yankin, Bulu Mammadu ya shaida wa BBC cewa an kai harin ne a garuruwan Ungumawo da Lamina da ke jihar Diffa.

Ya kara da cewa 'yan kungiyar sun cinna wa mata da yara wuta cikin gidaje, sannan suka kone wasu sassan garuruwan.

Ya yi kira ga hukumomin jihar su dauki kwakkwaran matakin dakile irin wadannan hare-haren.

Kasashen Nigeria da Nijar da Chadi da Kamaru da kuma Benin sun sha alwashin hada hannu wajen yaki da Boko Haram.