Matashi ya harbe mutane tara a Amurka

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Matashi ya kashe mutane tara a Amurka

Wani matashi wanda aka yi yakinin shekarun haihuwarsa ba su wuce 21 ba, ya bude wuta akan wata majama'a a garin Charleston da ke jihar South Carolina.

Tun dai da misalin karfe 9 na daren Laraba ne maharin ya je cocin wanda tana daya daga cikin majami'un da suka fi dadewa a kasar Amurka.

'Yan sanda jihar sun sanar da cewar harin yayi sanadiyar mutuwar masu bauta guda tara kuma wasu da dama sun jikkata.

Yanzu haka 'yan sandan sun bazama neman wanda ake zargi da yin kisan, wanda kuma aka ce wani matshi ne farar fata mai sanye da rigar sanyi da wata 'yar riga a kanta.