Ministocin kudi na Turai za su gana da Girka

Masu zanga-zanga kan batun bashi a Girka Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Masu zanga-zanga kan batun bashi a Girka

Ministocin kudi na Tarayyar Turai za su gana yau a birnin Luxemburg don tattauna batun shirin ceton Girka daga kangin bashi.

Muddin dai ba a cimma yarjejeniya ba, Girkar za ta iya baude ma shirin biyan bashin dake kan ta cikin kasa da makonni biyu masu zuwa - wannan kuma zai sanya a fitar da ita daga tsarin kudi na bai-daya na Tarayyar Turan.

Gabanin taron na Luxemburg, kasar ta Girka da hukumomin kasashen waje dake bin ta bashi, ba su da wata kwarin gwiwa cewar za a samu maslaha kan batun.

Jagoran Ministocin kudin na Tarayyar Turai ya ce damar da ake da ita ta cimma yarjejeniya kadan ce.

Karin bayani