Shugaba Jammeh ya zama 'Babili Mansa'

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Mr Jammeh ya shafe fiye da shekaru 20 a kan mulki

Shugaban kasar Gambia da ya fi kowanne dadewa a kan mulki, Yahya Jammeh ya samu karin mukamin da aka kara a cikin sunansa watau 'Babili Mansa'.

A harshen Mandika ma'anar sabon mukamin shi ne "Sadau" ko wanda "mai nasara".

Wata sanarwa daga fadar shugaban kasar, ta ce Mr Jammeh a yanzu za a dinga kiransa "His Excellency Sheikh Professor Alhaji Dr Yahya AJJ Jammeh Babili Mansa".

Jaridar Point ta ba da rahoton cewar a baya ya taba karbar mukamin a shekara ta 2014 amma kuma daga bisani bayan watanni hudu ya ajiye mukamin.

Shugaba Jammeh ya kwace mulki ne a shekarar 1994 kuma tun daga lokacin yake ta lashe zaben shugaban kasar da ake cece-kuce a kai.

A shekara ta 2011 ya shaidawa BBC cewa zai yi mulki na tsawon "shekara biliyan daya... idan Allah ya yarda".