Matashiya mai kyautar mota ta samu miji

Hakkin mallakar hoto Freedom radio
Image caption Zainab AbdulMalik, Matashiya mai kyautar mota da gida kudi ga duk wanda ya aure ta.

A ranar Laraba ne wata matashiyar nan da ta janyo cuncurundon daruruwan maza a jihar Kano a gidan rediyon Freedom da ke jihar ta zabi miji, bayan da ta yi alkawarin za ta bayar da mota da kudi da kuma gida ga duk wanda ya aure ta.

Wani ma'aikacin gidan rediyon Freedom ya ce "ta zabi saurayi guda kuma 'yan sanda sun dauke su tare sun tafi saboda basu kariya daga cincirindon mutane, amma sun rabuda da ita bayan sun fitar da su.

Matashiyar, Zainab Abdulmalik mai shekaru 22, ta bayyana aniyarta ne a wani sannanen shiri mai suna "In da Ranka", inda ta ce za ta bayar da wadannan kyaututuka ga duk wanda ya aure ta.

Matasa, wadanda suka kure adaka, daga sassan jihar sun yi tururuwa a ofishin gidan rediyon Freedom da ke unguwar Sharada.

Matashiyar ta bukaci duk matashi mai shekaru daga 17 zuwa 25 ya je gidan rediyon domin a tantance shi a ranar Laraba da safe.

Tun da misalin karfe 11 na safe matasa suka fara taruwa, a inda aka bukace su da su taru har sai da Zainab ta iso wurin da misalin karfe 1 na rana.

Zainab Abdul, 'yar asalin jihar Osun da ke kudu maso yammacin Najeriya, ta ce ta yi niyyar bayar da kyaututukan ne saboda tsohon saurayinta wanda suka kwashe tsawon shekaru suna tare ya yaudare ta.

Ta ce "Ni 'yar kasuwa ce a Kasuwar Singa kuma na kashewa tsohon saurayi na kusan naira miliyan biyar amma sai ya wulakanta ni duk da wadannan abubuwan da na yi masa. Saboda haka ne na je gidan radio domin bayar da sanarwar kyaututukan da zan bayar ga duk mai so ya aure ni. Bana tare da kowa kuma ban taba aure ba."