'Son zuciya ke jawo dumamar yanayi'

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Fafaroma Francis

Fafaroma Francis, cikin wani kundinsa a kan sauyin yanayi da aka dade ana dakonsa, ya ce son zuciya ne ke haddasa dumamar yanayi a duniya.

Bayanin kundin ya shafi mabiya darikar Katolika ne da al'ummar duniya baki daya, wanda a ciki Fafaroman ya bukaci attajirai da su sauya salon rayuwa, yana zargin cewa mutane ke bata kasa, kuma a karshe wahalar na karewa a kan talakawa.

Sai dai ya ce ba a makara ba wajen magance matsalar.

A bangare guda kuma wasu mabiya darikar Katolika da kuma 'yan jam'iyyar Republican a Amurka, sun soki wannan kundi na Fafaroma, suna cewa ya shiga fagen da ba nasa ba.