Shekarun balaga na tayar da cututtuka

Shekarun balaga
Image caption Shekarun balaga

Wani nazari da aka gudanar ya nuna cewar farkon shekarun balaga su kan zamo farkon samun cututtuka irin cutar sankara zuwa ciuwon suga.

Balaga tun a shekarun wuri ko kuma balagar lokacinda shekarun mutum suka ma zarce duk suna shafar yanayi dabam-dabam har 48 wanda ya hada da na gama haihuwa.

Nazarin da aka gudanar a kan kimanin mutane rabin miliyan wanda aka buga a rahoton masana kimiyya, ya nuna cewar balaga da kananan shekaru, yana kara kawo yiwuwar samun ciwon suga da kimanin hamsin bisa dari.

Masu binciken suka ce abin mamaki ne da balaga ke haifar da wani tasiri a kan lafiyar mutane a matsakaitan shekaru.

Tawagar likitocin daga Jami'ar Cambridge sun yi amfani da bayanai da aka tattara na bincike da dama da aka gudanar a kan lafiyar mutanen Brittaniya.

Wannan aiki ya dauki bayanan shekarun 'yan mata na jininsu na farko, to amma matakin farkon balagar yana da wuyar ganewa a tsakanin Maza, don haka suka nemi sanin ko sun balaga ne da wuri ko sai bayan wasu shekaru idan an kwatanta da sauran wasu takwarorinsu.

A tsakanin 'yan Mata, an bayyana cewa shekarun farko na balaga su kan kama ne daga shekaru 8 zuwa 11 yayinda wadanda suka balaga daga baya ta kan kama daga shekaru 15 zuwa 19.

Shekarun balaga na Maza dai ya kan kama ne tsakanin shekaru 9 zuwa 14 a cikin Yara.

Nazarin da aka yi ya nuna cewar balagar da wuri da kuma daga bisani duk suna haddasa wasu cututtuka kamar irinsu:- sankara da ciwon zuciya da ta mahaifa da hawan-jini da ciwon suga da ta kiba da dai sauransu.

Karin bayani