Malamai sun samu sabanin fahimta kan azumi

Image caption Masu azumi na bude baki

An samu sabanin fahimta a tsakanin wasu daga cikin malaman addinnin Musulunci game da azumin watan Ramadan a Biritaniya.

Wani shehun Malami a London, Dakta Usama Hasan, ya bayar da fatawar cewa saboda tsawon lokaci tsakanin fitowar alfijir zuwa faduwar rana, mutum zai iya bin Saudiyya wajen daukar azumi da shan ruwa ba wai sai ya shafe fiye da sa'o'i 19 ba.

A wannan yanayi na bazara a London wato Summer, rana na fitowa tun wurin karfe uku saura kwata sannan ta fadi wurin karfe tara da rabi.

Wani Malami a Jami'ar Coventry ta Biritaniya, Dakta Aliyu Musa, ya gaya wa BBC yadda ya ke kallon fatawar Dakta Hasan.

Dakta Aliyu ya ce "Mun sani cewa Allah SWT Ya fada a al-Kur'ani cewa Ya saukar da azumi ne saboda mu koyi tsoron Allah, in har mun duba lamarin ta wannan hanya za mu ga cewa maganar a rage lokacin shan ruwa bai ma taso ba."

Kazalika, ya kara da cewa "mutum zai ajiye azumi ne kawai a halin rashin lafiya ko na tafiya kamar yadda Ubangiji ya fada a littafi mai tsarki."

A duk lokacin da azumi ya fado cikin yanayin hunturu kuwa, to a kan yi azumin sa'o'i takwas ne kawai a Biritaniya.