Wasu 'yan uwa' sun tafi Syria domin shiga IS

Image caption A kwanakin baya ma wasu 'yan mata 'yan Biritaniya sun tafi Syria don shiga kungiyar IS

Wani mai fasa kwaurin mutane da ke da alaka da kungiyar IS ya ce wasu mata 'yan uwan juna uku tare da 'ya'yansu da suka bace a kan hanyarsu ta zuwa ibada Saudiyya daga Biritaniya sun tsallaka Syria.

Mai fasa kwaurin ya shaida wa BBC cewa mutanen sun kasu gida biyu ne, kafin su tsallake kan iyakar kasar Turkiya.

'Yan uwan da 'ya'yansu tara dukkansu 'yan birnin Bradford ne na Ingila.

Tuni dai mazajensu suka aika musu sakon rarrashin cikin hanya mai taba zuciya domin su dawo gida.