BH: EU za ta agaza da Euro miliyan 21

Hakkin mallakar hoto EPA
Image caption Shugaban kungiyar tarayyar Turai, Jean-Claude Junker

Tarrayar Turai wato EU ta yi alkawarin bayar da agajin kudi har Euro miliyan 21 don tallafa wa mutanen da rikicin Boko Haram ya shafa ta fuskar samar da abinci, da ruwan sha, da kuma muhalli.

Daga cikin wannan kudi dai, mutanen yankin arewa maso gabashin Najeriya za su samu Euro miliyan 12 da rabi, yayin da kuma za a bai wa al'ummomin kasashe makwabta da suka hada da Nijar da Kamaru da Chadi Euro milyan takwas da rabi.

A yau Juma'a ne ake sa ran kwamishinan na T.T mai kula da agaji da jinkai, Chritos Stylianides, zai gana da mataimakin shugaban kasar Najeriya, Yemi Osinbajo.

Kwomishinan dai na wata ziyara ne a Najeriya don gane wa idonsa irin barnar da rikicin Boko Haram ya haddasa.