An hana zartar hukuncin kisa a Pakistan

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Nawaz Sharif, Fira Ministan Pakistan

Firai minstan Pakistan, Nawaz Sharif, ya bai wa hukumomin kasar umarni su daina zartar da hukuncin kisa a lokacin azumin watan Ramadan.

Sanarwar ta bayyana cewa an dakatar da hakan ne saboda a girmama watan Ramadan, wanda aka fara a sassa daban-daban na Pakistan a ranar Juma'a.

A watan Disambar bara ne gwamnatin kasar ta dawo da zartar da hukuncin kisa wanda aka dakatar na tsawon bakwai a baya, domin mayar da martani a kan harin da kungiyar Taliban suka kai kan wata makaranta da ke garin Peshawar.

Tun daga lokacin, sama da mutane 170 aka kashe ta hanya rataye su, al'amarin ya janyo suka daga kungiyoyin kare hakin bil'adama.