Ana zargin wata da kashe mijinta

Hakkin mallakar hoto Nigeria Police website
Image caption Sifeton 'yan sanda Najeriya, Solomon Arase

Ana zargin wata mata da kashe mijinta a Kaduna cikin wani yanayi mai rudarwa.

Rundunar 'yan sandan jihar Kaduna ta ce, matar -- wacce ba a fadi sunanta ba -- ta hana matashin danta zuwa ya taimaki babansa lokacin da uban ke ihun neman taimako, daga wani daki da ake zaton matar ce ta kulleshi a ciki.

Mai laifin dai ta ki shaida wa 'yan sanda hanyar da ta bi wajen kashe mijin nata, amma 'yan sanda sun ce sun ji wari bilich na wanki mai karfi a dakin.

A yanzu haka matar tana tsare a hannun 'yan sanda domin ci gaba da bincike.