Dan-Maraya Jos ya rasu

Hakkin mallakar hoto Premiumtimes

Daya daga cikin shahararrun mawaka a Najeriya, Adamu Dan-Maraya Jos, ya rasu bayan ya kwashe fiye da shekaru 60 ya na waka a duniya.

Abokan arzikinsa sun ce ya rasu ne a asibiti a Jos bayan ya yi fama da rashin lafiya.

Daya daga cikinsu, Ladan Salihu, darakta-janar na Rediyon Tarayyan Najeriya ya ce ya rasu ne a ranar Asabar.

Daya daga cikin 'ya'yan da Dan-Marayan ya rike, Kucili Yusuf, ya ce marigayin mutum ne mai son jama'a sosai.

Dan-Maraya Jos ya yi suna sosai wajen yin wakokin da ke bayyana halin dan adam, wadanda suka hada harda wadda ya yi take 'Mutun Dan Adam Mai Wuyar Gane Hali".

Sunansa na asali shine Adamu Wayya, amma ana kiransa 'Dan-Maraya' ne saboda ya rasa mahaifansa tun yana karami.

Ya kware sosai wajen kidan kuntigi, kuma ya samu manyan kyaututtuka da yawa a ciki da wajen Najeriya saboda irin gudummuwar da wakokinsa suka bayar wajen neman zaman lafiya.

Tuni dai aka yi jana'izar marigayi Dan-Marayan ta hanyar da addinin Musulunci ya tanadar.