Alekos:Bankunan Girka ba zasu durkushe ba

Babban Bankin Turai Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Babban Bankin Turai

Flabouraris yace barin bankunan Girka su durkushe na iya shafar wasu bankunan a wasu kasashen Turai.

Yana magana ne a wani gidan talabijin din Girka kwana daya bayan babban bankin Turan ya kara yawan kudaden daukin gaggawa domin taimakawa bankunan Girkar cigaba da wanzuwa.

A makon da ya gabata masu ajiya suka fara kwashe biliyoyin kudaden su na euro daga bankunan.