Halittu na karewa a duniya - Bincike

Hakkin mallakar hoto Tibet forestry
Image caption Dabbobi na bacewa daga duniya

Masana kimiyya sun yi gargadin cewa an fara shiga kashi na shida na karewar halittu da ke kan doron-kasa.

Wani bincike da masana kimiyyar dabbobi suka yi ya lura cewa dabbobi na bacewa dari bisa dari cikin hanzari ba tare da wani matsatsi ba daga 'yan adam.

Masu binciken suka ce, bacewar halittun wadda ke da nasaba da lalacewar kasa da gurbatar muhalli da sauyin yanayi, suna faruwa cikin hanzari tun bayan bacewar kadangarun dinasours kimanin shekaru miliyan sittin da biyar da suka gabata.

Sai dai kuma nazarin ya yi kashedin cewa 'yan adam da kansu ne ke barazana ga rayuwarsu, don haka akwai alamun, za su iya zamowa halittu na gaba da za su bace daga doron kasa.