Burtaniya za ta sa hannu don kare al'adu

Image caption Firayiministan Burtaniya David Cameron

Gwamnatin Burtaniya ta ce za ta sanya hannu a wata muhimmiyar yarjejeniyar kasa da kasa ta kare kayayyakin al'adu a lokacin yake-yake.

A shekarar 1954 ne aka cimma yarjejeniyar bayan yakin duniya na biyu domin tabbatar da cewa kasashen duniya da sojoji ba zasu rika kai hari a wuraren tarihi dana adana kayayyakin al'adu a lokutan yaki.

Sai dai tun daga lokacin da aka cimma yarjejeniyar, Burtaniya bata sanya hannu a yarjejeniyar ba.

A shekarun 1990, yake yake a wasu yankunan kudu maso gabashin turai suka sa aka sake nazarin yarjejeniyar, sanna a shekarar 2004 Burtaniya ta ce zata sanya hannu a yarjejeniyar idan lokaci yayi.

Sabon sakataren kula da al'adu na Burtaniya, John Whittingdale ya ce a yanzu, yarjejeniyar zata zama wani bangare na dokokin kasar.

Ya ce barnar da kungiyar IS ta yi wa kayan tarihi a Syria da sauran wurare yasa Burtaniya taga daukan wannan mataki yana da muhimmanci.