Shugaba Buhari ya koma Aso Rock

Image caption Shugaba Buhari

Makonni uku bayan rantsar da shi, Shugaba Muhammadu Buhari na Najeriya ya tare a gidan Shugaban Kasa wato Aso Rock a ranar Lahadi

Tun lokacin da aka rantsar da shi, Shugaba Buhari da kuma mataimakinsa Yemi Osinbajo na gudanar da harkokin mulki ne daga gidajensu na kansu, da kuma 'Defense House' wanda ke unguwar Maitama a Abuja.

Wani mai taimakawa Shugaban Kasar kan harkokin yada labarai Femi Adeshina shi ne ya tabbatar da hakan a shafinsa na Twitter.

Tun a ranar Alhamis ne dai rahotanni suka ce maidakin Shugaba Muhammadu Buharin, Aisha Muhammadu Buhari ta koma gidan Shugaban kasar na Aso rock.